Jamio'in Asia sun samu ɗaukaka

Hakkin mallakar hoto harvard.edu
Image caption Jami'ar Harvard ita ce ta ɗaya a duniya

An samu ƙaruwar yawan jami'oin da ke nahiyar Asia da suka shiga jerin jami'oi mafiya inganci a duniya.

Yanzu dai jami'oi goma sha bakwai na nahiyar Asia ne suka shiga jerin jami'oi 100 da suka fi inganci a duniya a wannan shekarar da sashen ilimi na jaridar Times ke tantancewa.

Bara dai jami'oin nahiyar Asia goma ne kaɗai suke cikin jerin na gaba-gaba dari a duniya.

A karon farko, jami'ar Tsinghua da ke Beijing babban birnin China ta shiga wannan sahu, inda ta zama jami'a ta goma sha takwas a duniya.

Amma har yanzu jami'oin Amurka ne kan gaba a duniya inda jami'ar Harvard take cigaba da kasancewa ta daya a duniya.