Kamfanin Airbnb zai fadada harkokinsa

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kamfanin Airbnb na samar da masauki ga masu yawon bude-ido

Kamfanin Airbnb mai samar da masauki ga masu yawon bude-ido ya ce yana duba hanyoyin fadada kasuwancinsa.

Mai kamfanin Nathan Blecharczyk ya shaida wa BBC cewa masu yawon bude-ido na sha'awar sauka a gidajen mutanen da ba su saba da su ba da nufin kulla zumunci.

Mista Nathan Blecharczyk ya kara da cewa kamfaninsa na duba hanyar hada masu yawon-ido da masu sauke su a gidajensu ta yadda za su dace da juna wajen yin wasanni da sauran harkokin rayuwa.

A halin da ake ciki dai kamfanin yana da ofisoshi a birane dubu 34 da ke kasashe 191, kuma yana da darajar da ta kai dala biliyon 25.

Kamfanin Airbnb dai na taimakawa wajen ba wa mutane damar ba da hayar fili ko masauki a gidajensu ga masu yawon bude-ido ta hanyar tallata su ga masu bukata.

A cewar mai kamfanin, sun fahinci cewa masu yawon bude-ido da kuma masu ba su masauki na da kishirwar yin cudanya da mutane masu la'adu daban da nasu, wato mutane na bukatar walwala fiye da samun muhalli kadai.