Ba zan yarda a tsige ni daga mulki ba — Rousseff

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Ana zargin Misis Roussef da yin coge a asusun kasar.

brazilShugabar kasar Brazil, wacce ke fuskantar tsigewa daga wajen 'yan majalisar dokoki bisa zargin almundahana, Dilma Rousseff ta shaida wa BBC ba ta da laifin da ake zargin ta da aikatawa, don haka za ta yi bakin kokarinta don ganin ba a tsige ta daga kan mukaminta ba.

Ana zargin Misis Rousseff ne da yin coge a asusun gwamnatin kasar, inda ta boye wawagegen gibin da ke cikin asusun, sai dai ta musanta zargin.

Ta sha alwashin jajircewa don ganin ba a cire ta daga kan mulki ba.

A makon gobe ne majalisar dattawan kasar za a kada kuri'ar amincewa ko kin amincewa da shirin tsige shugabar ta Brazil.

Idan aka amince da shirin, za a dakatar da Misis Rousseff daga aiki tsawon kwana 180.

Kuri'ar jin ra'ayi da wata jaridar kasar ta gudanar ta nuna cewa 'yan majalisar dattawa 81 za su amince da shirin tsige shugabar.