Jami'an tsaro sun fafata da 'yan IS a kusa da Makkah

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Kungiyar ta IS ta ce ta kai hare-hare a yankuna da dama na kasar ta Saudiyya.

Rahotanni daga kasar Saudiyya sun ce jami'an tsaron kasar sun yi ba-ta-kashi da mayakan kungiyar IS a wajen birnin Makkah.

Wasu rahotanni sun ce jami'an tsaron sun yi nasarar murkushe 'yan kungiyar ta IS.

An kashe akalla dan kungiyar ta IS guda daya.

A cikin shekara guda dai, kungiyar ta IS ta ce ta kai hare-hare a yankuna da dama na kasar ta Saudiyya, ciki har da harin da ta kai wasu masallatan 'yan Shi'a.

Hukumomin kasar sun kaddamar da sababbin matakai na hukunta duk wanda ya tafi kasashen Syria ko Iraqi domin nuna goyon baya ga IS.