An yi jana'izar ɗaliban Kano

A jihar Kano da ke arewacin Najeriya an yi jana'izar ɗaliban nan shida 'yan makarantar sakandare da malaminsu waɗanda suka yi haɗari a hanyar Lagos.

Haɗarin dai ya faru ne yayin da ɗaliban suke kan hanyar komawa gida, bayan sun halarci wata gasar kacici-kacici a jihar Lagos.

An dai yi wa mamatan sutura ne gaba ɗayansu, sannan aka yi musu jana'iza kuma aka binne su waje guda, ƙarƙashin jagorancin gwamnan jihar Kano.

An yi wa ɗaliban da jagoransu da kuma direbansu sallah a kofar fadar Sarkin Kano, jana'izar da ta samu halartar dubban jama'a da suka haɗa da 'yan uwa da jami'an gwamnati da kuma sauran masu tausayawa.

Bayan kammala sallar ne kuma aka binnesu a maƙabatar Tarauni, inda aka yi musu kaburbura a jere kusa da juna.

Tun gabanin jana'izar mutanen dai, sai da gwamnan Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya gana da iyayen ɗaliban, ya sanar da su mutuwar 'ya'yansu a hukumance, sannan ya nemi izininsu na cewa gwamnati ta ɗauki ɗawainiyar yi musu sutura tare da wakilcin iyayen, abinda kuma suka amince.

Tuni dai gwamnan Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya miƙa sakon ta'aziyyar gwamnati ga iyayen yaran da suka rasa rayukansu a haɗarin.

Bayanai dai sun nuna cewa ɗaliban da suka mutu su shida ne, uku daga cikinsu daga makarantar haɗaka ta Ƙaraye, uku kuma daga makarantar sakandaren gwamnati ta Kano capital, sai kuma jagoransu, da kuma direban motar.

Haɗarin ya faru ne sakamakon fashewar tayar motar da suke ciki.