Kenya: An gano mai rai a kasan gini bayan kwana 6

An gano wata mata da ranta bayan kwana shidda da ruftawar wani dogon gini a Nairobi, babban birnin kasar Kenya.

Masu aikin ceto sun ce sun yi ta tattaunawa da matar domin tsara hanyoyin da za a cetota.

A kalla mutane 33 ne aka tabbatar da cewa sun mutu a ranar Juma'a, bayan ruftawar ginin benen mai hawa shida, ana kuma neman fiye da mutane 80 har yanzu.

Wani rahoto da kamfanin dillanci labarai na AP ya fitar, ya ce shugaban hukumar kai agajin gaggawa, Pius Masai, ya ce an bai wa matar allurar gulukos, kuma tana cikin koshin lafiya.

Kotu dai ta bayar da belin masu ginin, wadanda aka kama ranar Litinin.