Me ka sani kan rikicin fulani da manoma a Nigeria?

Bayan zarge-zarge da ake yi wa makiyaya Fulani a Nigeria kan hare-haren da aka kai wa wasau al'ummun kasar a wannan shekarar, shugaban Najeriyar ya bai wa sojin kasar umarnin su magance matsalar da gaggawa.

Sai dai ba wani sabon abu ba ne, rikice-rikice tsakanin makiyaya Fulani da manoma ya yi sanadiyar mutuwar dubban 'yan Najeriya a shekaru 20 da suka wuce.

A cewar wani rahoton alkaluman 'yan ta'adda na duniya da aka fitar a shekarar 2014, sama da mutane 1,200 ne suka rasa rayukansu. Hakan ne ma ya sa Fulanin suka zama 'yan ta'addar da suka fi ɓarna a duniya.

Kisan mutane 300 da aka yi a watan Fabrairu a jihar Benue da kuma harin da aka kai kudancin Enugu, inda aka kashe sama da mutane 40, ya tayar da jiyoyin wuya a Najeriya. An lalata gidaje kuma an tirsasawa dubban mutane barin muhallansu.

Wannan ya ƙara sanya ƙiyayyar ƙabilar Fulani a wasu wurare na ƙasar, inda aka samar da maudu'in #fulaniherdsmen wanda ke nufin #makiyayafulani ya kuma ja hankali sosai a shafukan sada zumunta da muhawara.

Shugaba Muhammadu Buhari, wanda shi ma bafullatani ne, ya mayar da martani a kan koken da mutane ke yi a kan batun kuma ya buƙaci sojojin ƙasar su daƙile hare-haren.

Sai dai kuma lamarin yana da sarƙaƙiya.

*Tana daga cikin ƙungiyar makiyaye mafi girma a duniya kuma ana samun su a yammaci da kuma yankin tsakiyar Afrika, daga Senegal zuwa jamhuriyar Tsakiyar Afrika.

*A Najeriya wasu sun cigaba da zama a matsayinsu na makiyaya, yayin da wasu suka koma birane.

*Fulani makiyaya suna yin akasarin rayuwarsu a daji ne, ba kamar mutanen da ke zama a cikin birane ba, kuma suna da alaƙa da waɗannan rikice-rikicen.

* Suna kiwon dabbobinsu a yankuna da dama, inda suke yawan yin rikici da al'ummomin da galibin aikinsu noma ne.

*Ana yawan dangantasu da ƙabilar Hausa, saboda tsawon lokacin da suka shafe suna zaman tare.

*Fulani sun taka muhimmiyar rawa a ƙarni na19 wajen farfaɗo da addinin Musulunci a Najeriya.

Me ke kawo rikicin?

Ana tunanin ce-ce-ku-ce a kan abubuwan more rayuwa kamar su gonaki da yankunan da ke da burtali da ruwa ne ke jawo rikici tsakanin makiyaya da kuma manoma.

Fulani makiyaya kan iya tafiya mai nisa tare da dabbobinsu domin nema musu abinci. Mafi yawan lokuta, suna daukar makamai domin kare dabbobin nasu.

Suna yawan rikici da manoma wadanda ke yawan cewa suna lalata musu amfanin gona kuma basa kula da inda dabbobin nasu ke zuwa.

Fulanin na zargin cewa manoma waɗanda ke ƙoƙarin satar shanunsu -- suna ƙoƙarin kare kansu ne.

A da, rikicin a yankin tsakiyar Najeriya aka fi yi, inda kiristoci ƙabilar Birom da ke jihar Plateau suke kisan ramuwar gayya ga Musulmai da makiyaya.

Yadda sauyin yanayi ya ke shafar burtali ya sa Fulani makiyaya sun kara matsawa zuwa kudancin Najeriya domin neman ruwa da ciyawa.

Wannan ya ƙara faɗaɗa rikicin ta inda ake cigaba da fuskantar munanan tashe-tashen hankula a kudancin ƙasar, ana ƙara jin tsoron cewar rikicin zai yi barazana ga haɗin kan da dama ya ke tangal-tangal tsakanin ƙabilun Najeriya.

Me yasa rikicin ke da sarƙaƙiya?

Bayan rikice-rikice da manoma, ana zargin cewa Fulani suna fashi da makami, da fyade da kuma rikicin ƙabilanci, musamman a yankunan tsakiya da kuma arewacin Najeriya. An yi wasu zargin masu kama da haka a kan Fulani a ƙasar Ghana da Ivory Coast.

Alaƙarsu da Hausawa da kuma yanayinsu ya sa suna fuskantar haɗarin kai musu hare-hare, kuma sun tsinci kansu a cikin rikici wanda basu da masaniya a kai.

Akasarin rikice-rikicen yankin tsakiyar Najeriya sun fara ne tun shekarar 2002, da kuma rikicin yankin Yelwa-Shendam na jihar Plateau da ya yi sanadiyar mutuwar dubban mutane.

Wannan ya kawo rikice-rikicen ƙabilanci da na siyasa da tattalin arziƙi da kuma na addini.

A baya-bayan nan ne dai 'yan sanda suka sanar da kamen wasu Fulani masu ɗauke da makamai da dama a wajen Abuja. Mutanen sun ce suna hanyarsu ta gano shanunsu ne da aka sace.

Ƙungiyoyin Fulani sun sha musanta alaƙarsu da masu tayar da ƙayar baya inda suka ce ana yi musu ƙazafi ne kawai.

Sa'idu Baso, wani shugaban Fulani a kudancin Najeriya, ya shaida wa BBC cewar, ''Bai dace ana yi mana ƙazafi a kan duk wani abu da ya faru ba, saboda a wasu lokutan mu ma abin yana shafarmu.''

Daga ina suke samo makaman?

Munin rikicin ya sa mutane na tunanin inda ake samun makaman da ake kai harin da su.

Wani tsohon kwamishinan 'yan sanda na ƙasa ya shaida wa BBC cewa makamin da aka fi amfani da shi wajen wannan rikicin shi ne bindiga kirar AK47.

Ya ƙara da cewa rikin Libiya da na Mali ya ƙara yawan yaɗuwar ƙanana da kuma manyan makamai a yankin kudu da hamadar sahara musamman Najeriya, saboda babu isasshen tsaron kan iyakokinta.

Yaya girman rikicin yake?

Ƙungiyar bayar da agaji da ke Biritaniya, Mercy Corps, ta ce rikicin ya sa Najeriya ta yi asarar dala biliyan 14 a shekara uku.

Hare-haren wata sabuwar barazana ce ga tsaro a ƙasar da ta shafe shekara bakwai tana fama da rikicin ƙungiyar Boko Haram a arewa-maso gabahin ƙasar.

Majalisar ɗinkin duniya ta ce ta damu sosai da ƙetar da maharan ke nunawa sannan kuma ta yi kira ga gwamnati da ta ƙara ƙoƙari wajen kare 'yan kasarta.

'Yan majalisar ƙasar na aiki a kan samar da dokar da za ta samar da burtali a sassan Najeriya domin kawar da rikicin tsakanin ɓangarorin biyu.

Sai dai yunkurin nasu bai samu karɓuwa ba a wajen mutane, musamman a kudancin ƙasar.

Zai yi wahala a yi jam'in duk wasu abubuwa da ya danganci Fulani, saboda mafi yawan lokuta waɗannan makiyayan ba su ma san junansu ba kuma suna tafiyar da al'amuransu ba tare da dogara da kowa ba.

Ko shakka babu na cewar babu wata shaidar da ta nuna cewar ƙungiyar Fulani tana da wata manufa ta siyasa.

A don haka ba dai-dai ba ne a bayyana su a matsayin ƙungiyar 'yan ta'adda.

Wannan ne ya sa zai yi wuya hukumomi su samar da shirin da zai kawo ƙarshen wannan rikicin.