North Korea: Workers Party na babban taro

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ana sa rai shugaban kasar zai jaddada shirin nukiliyar kasar a cikin jawabin nasa.

A Kasar Koriya ta arewa, an fara babban taron jam'iyyar Workers Party mai mulkin kasar a Pyongyang, a karon farko cikin shekara 36 da suka wuce.

Dubban wakilan jam'iyyar ne suka halarci wajen taron wanda za a kwashe kwana hudu ana yi, taron da ake sa ran shugaban kasar, Kim Jong-un zai yi amfani da shi wajen bayana matsayin gwamnatinsa a kan wasu al'amura.

Ana dai sa ran shugaban kasar zai jaddada shirin nukiliyar kasar a cikin jawabin nasa, kuma ana ta yada jita-jitar cewa watakila kasar za ta yi gwajin makamin nukiliya kashi na biyar a lokacin taron.

Kimanin 'yan jarida 100 ne daga kasashe waje aka gayyata zuwa wajen taron.

Sai dai wakilin BBC ya ce ba a kyale su sun shiga dandalin da ake taron ba ballatana su ji jawabin shugaban kasar.

Yanayin da aka tashi dashi a kasar ba zai yiwa taron da dubban wakilan jam'iyyar suka halarta dadi ba, saboda an tashi da mamakon ruwan sama da tsawa.