Jonathan zai iya faɗa da kowa a kan Diezani — Sanusi

Hakkin mallakar hoto cbn website
Image caption An dakatar da Sanusi Lamido Sanusi daga shugabancin babban bankin Najeriya bayan ya fallasa barnar da ma'aikatar man fetur ke yi.

Mai martaba Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya ce tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan zai iya korar kowa daga kan mukaminsa idan ya aibata tsohuwar ministar man fetur Diezani Allison-Madueke.

Sarki Sanusi II, wanda ya bayyana haka a wata hira da ya yi da gidan talabijin na Forbes Africa, ya kara da cewa sanin haka ne ya sa ya shirya sauka daga mukaminsa na shugaban babban bankin kasar, a lokacin da ya kai karar ta wajen shugaban kasar.

Tsohon shugaban babban bankin na Najeriya dai ya aikewa Goodluck Jonathan wasika, inda ya shaida masa cewa ma'aikatar man fetur ba ta sanya Dala Biliyan 49 na kudin man da ta sayar ba amma tsohon shugaban kasar bai ce masa komai a kai ba.

A cewar Sarki Sanusi II, Goodluck Jonathan ya yi magana a kan batun ne kawai sakamakon wasikar da tsohon shugaban kasar Cif Olusegun Obasanjo ya rubuta wasa, wacce aka wallafa a jaridu da dama na kasar, inda ya bukace shi ya dauki mataki a kan zarge-zargen satar da ake yi a ma'aiakatar man fetur.

A wancan lokacin, batun kin saka kudin a babban bankin na Najeriya ya tayar da jijiyoyin wuya, lamarin da daga karshe, ya kai ga dakatar da Sarki Sanusi II daga shugabancin babban bankin kasar.