An kai hari kan sansanin 'yan gudun hijra a Syria

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption An kashe mutane akalla talatin a sansanin 'yan gudun hijra a Syria

An yi amanna cewa wani hari ta sama da aka kai kan wani sansanin 'yan gudun hijra da ke kusa da iyakar kasar Turkiyya ya hallaka mutane akalla talatin.

Har yanzu ba a san ko waye ya kai harin ba, sai dai kuma wani dan jarida da ke yankin ya shaidawa BBC cewa ana zargin sojojin Syria ne wadanda ke kai wa 'yan tawaye hari a makonnin nan ne suka kai harin.

Dan jaridan Kareem Shaheen ya ce an lalata wani bangare mai girma wanda ya kunshi gidajen mutanen da suka taho daga birnin Aleppo.

Ya bayyana lamarin da cewa bai yi da di ba saboda an kona tantuna da dama da mutane ke zama a ciki.

Fadar White house ta Amurka ta yi Allah wadai da harin.

Mai magana da yawun fadar, Josh Earnest ya ce bai kamata ana kai irin wadannan hare-hare ta sama kan farar hular da ba suji ba su gani ba, wadanda suka tsere wa rikici.