Kamfanonin tura sakonnin E-mail na bincike

Hakkin mallakar hoto SCIENCE PHOTO LIBRARY

Kamfanonin tura sakonni na E-mail na bincike kan wani rahoton dake cewa masu satar bayanan jama'a da muguwar manufa na samun bayanan miliyoyin masu tura sako ta Internet.

Kamfanonin da yanzu haka suka dukufa wajan binciken wannan batu sun hada da Gmail da Hotmail.

Kamfanonin da lamarin ya shafa kuma sun hada da Google Gmail, da Yahoo Mail, da Microsoft Hotmail da kuma Mail.ru.

Rahoton ya gano cewa a baya babu irin badakallarnan ta sanin kalmomin siri da mutane ke amfani da su a akwatunan su na tura sakonni.

An dai gano sakonni milyan 272 da kuma kalmomin siri sama da milyan 42 da masu satar bayanai ko sakonni don yaudara suka samu.