Buhari ya sanya hannu kan kasafin kudin 2016

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption An yi takun-saka tsakanin fadar shugaban kasa da 'yan majalisar dokokin Najeriya kan kasafin kudin.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sanya hannu a kan kasafin kuɗin ƙasar na 2016 wanda aka yi ta cece-kuce a kansa.

Shugaban ya sanya hannu kan kasafin kuɗin ne a yayin wani ƙwarya-ƙwaryan taro da aka yi a fadar shugaban Nigeria da ke Abuja, babban birnin ƙasar.

Mutanen da suka shaida wannan lamari sun haɗa da mataimakin shugaban ƙasa Farafesa Yemi Osinbajo, da shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki, da kakakin majalisar wakilai Yakubu Dogara, da shugaban jam'iyyar APC John Odigie-Oyegun, da shugabannin kwamitin kasafin kuɗi na majalisar dokokin ƙasar.

Akwai kuma ministar kudi ta ƙasar Kemi Adeosun, da babban mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan al'amuran majalisar dattawa Ita Enang, da kuma babban mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan al'amuran majalisar wakilai Sama'ila Kawu Sumaila.

'Takun-saka'

Tun a watan Disambar shekarar 2015 ne shugaban ƙasar ya miƙa kasafin ƙudin ga majalisar dattawa.

Sai dai daga baya an yi ta kai ruwa rana tsakanin fadar shugaban ƙasa da majalisar dokokin kan abin da ke ƙunshe cikin kasafin ƙudin, al'amarin da har ya jawo shugaba Buhari ya ƙi sanya hannu da wuri yana mai cewa sai an bashi cikakken bayanin kasafin kamar yadda ya aikewa majalisar.

Rashin sanya hannu da wuri kan wannan kasafi dai ya jawo ce-ce-ku-ce a Najeriya, inda har mutane da dama ke ganin halin ha'u'la'in da ake ciki a ƙasar kamar tsadar rayuwa da sauran abubuwa na da alaƙa da rashin wanzar da kasafin.

A yanzu dai a iya cewa sa hannun shugaban ƙasa kan wannan kasafi zai kawo sauƙin al'amuran da suka shafi rayuwar al'umma.