Mara hannu ta ci gasar masu hannu

Hakkin mallakar hoto zanerbloser

Wata yarinya 'yar shekara bakwai da aka haifa babu hannu ta lashe gasar iya rubutu na kasa da aka gudanar a Amurka.

Anaya Ellick, wacce 'yar asalin Chesapeake ce da ke jihar Virginia, ba ta amfani da hannun roba, saboda haka in dai za ta yi rubutu sai dai ta karkata abin rubutun da dungulmin gabobin nata biyu.

Tracy Cox ce shugabar makarantar Greenbrier Christian Academy, inda Anaya ke karatu, ta ce wannan tamkar ishara ce ga al'umma.

Ta ce, "Bata bari komai ya dauke mata hankali game da abin da ke gabanta ba."

Cox ta kara da cewa, "Tana da hazaka, kuma tana cikin wadanda suka fi iya rubutu a ajinta."

Rahotanni sun ce yarinyar dai ta bige yara 50 a gasar, domin samun nasarar shiga sashen masu matsala a gasar iya rubutu ta kasa, inda ake son kyautata wa daliban da ke da matsaloli da ke da alaka da kwakwalwa ko gabar jiki ko kuma rashin fahimtar karatu.

Daraktar gasar Kathleen Wright, ta shaida wa tashar labaran ABC cewa, rubutun da Anaya ta yi tamkar wanda ke da hannu ne ya rubuta.

Hakkin mallakar hoto Greenbrier Christian Academy
Ga yadda tsarin gasar yake:

Kamfanin Zaner-Bloser ya shirya gasar, kuma ya ce ya tsara ta ne ta yadda kowanne dalibi zai samu dala 1,000.

Sun saka hoton yarinyar da ta ci gasar rike da kambunta a shafinsu na twitter.

Ga Jessica Cox mai shekaru 30 ma bata bari rashin hannu ya hana ta zamowa matukiyar jirgi ba.

A shekarar 2013, BBC ta fitar da rahoto da ya zamo wa mutane da dama darasi, ganin yadda ita ma an haife ta ba tare da hannu ba amma hakan bai hana ta tuka mota, ko jirgi ko ma latsa Piano ba.