Nigeria:Rikici tsakanin kungiyar kwadago da gwamnati a Kaduna

Image caption Rikici tsakanin kungiyar kwadago da gwamnatin jihar Kaduna

A Najeriya, takaddama ta kaure tsakanin gwamnatin jihar Kaduna da kungiyar Kwadago sakamakon matakin da gwamnati ta dauka na ba wa ma'aikata zabi kafin a cire bangaren albashinsu a matsayin gudunmuwa ga kungiyar kwadago.

Gwamnatin jihar dai ta ce dokar kasa ta ba wa ma'aikaci zabin shiga kungiyar ko akasin haka.

Sai dai Kungiyar kwadago a nata bangaren ta bayyana matakin a matsayin katsalandan.

Comrade Adamu Ango shi ne shugaban kungiyar kwadagon reshen jihar Kaduna, ya ce doka bata bawa bangaren gwamnati hurumin binciken yadda ake kashe kudin kungiya ba, ko kuma hana ma'aikata shiga kungiya.

Har yanzu dai kungiyoyin ma'aikata a jihar ba su amince da hanzarin gwamnatin ba.