An kashe mutum 70 a Aleppo

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption An kai hari a kusa da Aleppo ne duk da yarjejeniyar tsagaita wutar da aka amince da ita.

Masu fafutika a Syria sun ce an kashe akalla mutum 70 a sabon fadan da ya barke a wani kauye da ke yammacin birnin Aleppo duk da yarjejeniyar tsagaita wutar da aka amince da ita.

Kungiyar kare hakkin dan adam ta Syrian Observatory for Human Rights, wacce ke da mazauni a Biritaniya, ta ce mayakan kungiyar Nusra Front sun sake kwace garin Khan Touman daga hannun dakarun gwamnati.

Tun da farko dai, sai da wani babban jami'in majalisar dinkin duniya ya ce harin da aka kai ta sama a kan sansanin masu gudun hijira a Syria, wanda ya yi sanadin mutuwar akalla mutum 30, ka iya zama laifin yaki.

Jami'in da ke kula da ayyukan jinkai na majalisar dinkin duniyar Stephen O'Brien ya bukaci a gudanar da bincike a kan harin, wanda aka kai a lardin Idlib da ke kusa da iyakar Syria da Turkiyya.

Mazauna yankin dai na zargin gwamnatin Syria da kai harin, kasancewar ta kai hari a kan 'yan tawayen da ke yankin a cikin 'yan makwannin da suka wuce.

Sai dai gwamnati ta musanta zargin.