A ina Fulani ke samun makamai?

Image caption Rikicin Fulani da makiyaya na kara kamari a Najeriya

Yawaitar rikici tsakanin Fulani da makiyaya da manoma a wasu sassan Najeriya ya sa mutane suna tunanin a ina Fulanin waɗanda su aka fi zargi da kai hare-hare ke samun makaman.

Wani tsohon kwamishinan 'yan sanda na ƙasa Abubakar Tsav, ya shaida wa BBC cewa, makamin da aka fi amfani da shi wajen wannan rikicin shi ne bindiga kirar AK47.

Ya ƙara da cewa rikicin Libiya da na Mali ne ya ƙara yawan yaɗuwar ƙanana da kuma manyan makamai a yankin kudu da hamadar sahara musamman Najeriya, saboda babu isasshen tsaron kan iyakokinta.

Ya ce, ''Wasu mutanen na musayar ɗanyen man fetur domin a basu makamai kuma fitar da su na da matuƙar sauƙi ta tasoshin jirage ruwanmu.''

Wani hasashen kuma shine ana ganin suna sayen makaman ne a ƙasashen da ke yammaci da tsakiyar Afrika, kasancewarsu masu yin doguwar tafiya ta daji zuwa ƙasashe daban-daban na yankin.

Ganin yadda hare-haren suke ƙara yawaita ne ya sa shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bai wa hukumomin tsaron ƙAsar umarni yin maganin duk wanda aka kama da laifin.

Karin bayani