Za a gudanar da zabe a watan Yuni a Australia

Image caption Malcolm Turnbull ya ce za a gudanar da zaben kasarsa a watan Yuni mai zuwa

Firayim Ministan Australia, Malcolm Turnbull ya ce kasarsa za ta gudanar da babban zabe a ranar 2 ga watan Yulin wannan shekarar.

Tuni dai aka rusa majalisun dokokin kasar gabannin zaben, lokacin da Mr Turnbull zai nemi tsayawa takara, wato wata takwas kenan da yi wa wanda ya gabace shi, wato Tony Abbott juyin-mulki amma a matakin jam'iyya.

Jam'iyyar Mr Turnbull ta Liberal Party dai na fatan sake kafa gwamnati, duk kuwa da matsalar da ake fama da ita ta tabarbarewar tattalin arziki sakamakon faduwar farashin tama da gawayin Kwal, wanda kasar ta dogara da shi wajen samun kudin-shiga.