An kama wani kwamanadan yan tawayen FDLR

Hakkin mallakar hoto

Hukumomi a Jamuhuriyar Dimokradiyyar Kongo sun ce sun kama mataimakin kwamandan kungiyar 'yan tawaye da ke da alaka da kisan kiyashin da aka yi a Rwanda a 1994.

Mai magana da yawun gwamnatin yace an kama Janar Leopold Mujambere na kungiyar FDLR a birnin Goma da ke gabashin kasar.

Kungiyar FDLR ta kunshi yan kabilar Hutus ne wadanda aka zarga da kashe dubban daruruwan 'yan Tutsi da kuma 'yan Hutu masu sassaucin ra'ayi a lokacin kisan kiyashin Rwanda.

Rwandan dai ta sha kai harin soji a gabashin Kongo a yunkurin murkushe kungiyar ta FDLR