Za a dakatar da bayar da matsugunni ga baki a Kenya

Hakkin mallakar hoto
Image caption Kenya zata daina bawa baki matsugunni

Bayan shekaru ashirin da biyar da samarwa 'yan kasashen Somalia da Sudan ta Kudu mafaka , gwamnatin Kenya ta ce nan ba da jimawa ba za ta dakatar da tsarin bayar da matsuguni ga bakin da suka fito daga kasashe makwabta.

A ranar juma'ar data wuce ne gwamnatin kasar ta rufe hukumar kula da 'yan gudun hijira ta kasar kuma ta ce nan bada jimawa zata rufe sansanin' yan gudun hijira da ke Dadaab da kuma Kakuma wadanda yan gudun hijira 600.000 ke samun mafaka.

Kakakin ma'aikatar cikin gida na kasar ta Kenya Mwenda Njoka ya ce babbar barazana ce matsalar 'yan gudun hijra musamman idan aka yi la'akari da cewa ba su taba fuskantar irin wannan matsala ta 'yan gudun hijra da ke sansanoni kamar irin matsalolin da suka fuskanta a shekarun baya-bayan nan.

Kazalika matsalar ta 'yan gudun hijra na da alaka da ta'addanci, kuma gwamnati ta dade ta na nazari a kan yadda zata bullowa lamarin, dan haka a wannan karon da gaske muke.