An kama masu satar mutane 6 a Kaduna

Hakkin mallakar hoto Nigeria Police website

Rundunar yansandan Najeriya ta ce, tawagar jami'an farin kayanta ta musamman ta tarwatsa gungun masu satar mutane a jihar Kaduna.

A wata sanarwa da ta fitar rundunar ta ce yanzu haka an cafke shidda daga cikin su da suka hada da jagoran kungiyar Kashimu Shehu da aka fi sani da Baliago.

Sauran su ne Aliyu Mato da aka fi sani da yellow, da Muhammedu Mamman, da Hassan Bello, da Bala Mohammed, da kuma Ishiaku Kabiru.

Rundunar ta ce nan ba da jimawa ba za a gurfanar da wadanda ake zargin da satar mutane a yankunan Kaduna da Zaria a gaban kotu.

Ta kuma bayyana cewa ana zargin mutanen da hannu wajen satar wasu limaman kirista a kauyen Dutse a jihar Kaduna, da suka hada da Rev Illiya Anthony wanda ya rasa ransa yayin da yake tsare a hannun su.

Babban sipeton yansandan Najeriyar Solomon Arase ya ce ana cigaba da farautar sauran 'yan kungiyar da suka tsere.