Ana cigaba da aikin ceto mutane a hatsarin Jebba

Hukumar kiyaye hadura a Najeriya ta ce ma'aikatanta da jamian 'yan sanda suna ci gaba da aikin ceto mutanen da suka makale a hatsarin jirgin kasa da ya faru a garin Jebba da ke jihar Kwara

Jirgin kasa na dakon kaya ya tashi daga Lagos zuwa Kano ya goce ne daga kan layin dogo a garin Jebba.

Kakakin hukumar kiyaye hadura Bisi Kazeen ya shaidawa BBC cewa a halin yanzu an tura mai dauke da na'ura da kugiya zuwa domin ta dauko taragun da ya fada akan mutanen da ke cikin jirgin

Ya kuma ce mutane biyu ne suka mutu ya yinda uku suka ji raunuka.

Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne sakamakon lalacewar birki.

A Najeriya dai ana fama da asarar dimbin rayukan jama'a a kowace shekara, sakamakon hadarin ababen hawa, kama daga babura zuwa motoci, inda mahukunta ke danganta hadarin da tukin ganganci ko rashin kula da lafiyar ababen hawa.