An saki 'yan jaridar Spaniya uku da aka sace

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption An sace 'yan jaridar ne watanni goma da suka gabata.

An sake wasu 'yan jarida uku 'yan kasar Spaniya, wadanda aka sace a Syria watanni goma da suka wuce.

An dai yi musu ganin karshe ne a Aleppo, lokacin da suke aika rahotanni a kan yakin da ake yi a birnin, a watan Yulin bara.

Jaridar El pais ta kasar Spaniya ta ce a halin da ake ciki, 'yan jarida ukun, wato da Antonio Pampliega, da Hose Manuel Lopez da kuma Angel Sastre suna kasar Turkiyya, suna shirin komawa gida.

Gwamnatin Spaniya ta ce kasashen Qatar da Turkiyya sun taka muhimmiyar rawa wajen ceton 'yan jaridar.