Mutum 73 sun mutu a hadarin mota a Kabul

Hakkin mallakar hoto

Jami'ai a kasar Afghanistan sun ce mutane 73 ne suka mutu lokacin da wadasu motocin safa biyu suka yi karo da wata motar daukar mai.

Mutane da dama sun ji raunuka a hatsarin wanda ya faru a babban titin da ya hada Kabul da garin Kandahar a kudancin kasar.

Duk motocin uku sun kama da wuta .

Afghanistan kasa ce da ke fama da yawan hadurran motoci saboda rashin kyawun hanyoyi da kuma rashin aiwatar da dokokin kiayaye hadurra.

Mohammadullah Ahmadi, daraktan hukumar kula da hanyoyi a gundumar, ya ce tukin ganganci ne ya haddasa hadarin.

Kakakin ma'aikatar lafiya ta kasar, Ismail Kawasi, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa yawancin wadanda suka mutu a hadarin sun kone kurmus.

A nasa bangaren, mai magana da yawun gwamnan gabashin gundumar Ghazni ya shaida wa BBC cewa ya ga takardu da suka nuna cewa baki daya fasinjoji 125 ne suke tafiya a cikin motocin bas-bas din guda biyu.

Karin bayani