Koriya ta kudu ta yi watsi da tayin Koriya ta arewa na sasantawa

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Koriya ta kudu ta ce neman sulhun da koriya ta arewa ke yi dadin baki ne

Koriya ta kudu ta yi watsi da tayin da makwabciyarta Koriya ta arewa ta mata cewa ya kamata su hau teburin sulhu da cewa dadin-baki ne da yaudara kawai.

Koriya ta kudun dai na maida martani ne ga kalaman da shugaban Koriya ta arewa, Kim Jong-un ya yi a wajen babban taron jam'iyyarsa ta Workers Party a ranar Asabar din da ta gabata, inda ya ce ya kamata kasashe biyun su gana don rage yawan zaman-doya-da-manjan da suke yi da juna.

Wakilin BBC da ya kai ziyara Koriya ta arewa ya ce dukkan kasashe biyun sun saba da tada-kura a tsakanin junansu da nufin tauna-tsakuwa don aya ta ji tsoro.

Ko da a baya-bayan nan Koriya ta kudu, tare da hadin-gwiwa da Amurka ta yi wani atisayin sojoji, yayin da Koriya ta arewa ta jarraba wani makaminta na nukiliya.