Direbobin Nigeria sun koka kan haraji

Kungiyar kananan direbobin manyan motoci da ke dakon man fetur da manyan kaya a Najeriya ta ce ta gana da wasu daga cikin hukumomin yankin kudu-maso-yammacin kasar game da karbar haraji barkatai da ake yi a hannunsu.

Kungiyar ta kuma bukaci gwamnatocin jihohin Oyo, da Ondo, da Ekiti, da Osun da kuma Legas da su gargadi wasu jami'an tsaro da wasu da ta kira tsageru, wadanda ta ce suna cin su tara da kashe membobinsu a kan hanya.

Direbobin sun ce kara wa'adin zama ga mahukuntan zai zamo na karshe, muddin kuma basu samu biyan bukata ba, to kada a zarge su da yiwa Najeriya zagon kasa ta bangaren karancin kayayyakin masarufi zuwa kudancin kasar da kuma dakon mai daga Lagos zuwa wasu yankunan Najeriya.

Kazalika kungiyar ta yi barazanar cewa za ta shiga yajin aiki muddin ba a samu sauyi ba.