An kashe wani dan Jarida mai fafutuka a Karachi

Hakkin mallakar hoto Reuters

An kashe wani fitaccen dan Jaridar Pakistan kuma mai fafutukar kare hakkin dan Adam Khurram Zaki a birnin Karachi.

Mr Zaki yana cin abinci ne a wani gidan abinci da ke gefen hanya lokacin da wasu 'yan bindiga a kan Babura biyu suka bude masa wuta.

Wata kungiyar da ta balle 'yan Taliban a Pakistan ta ce ita ce ta kai harin saboda adawar da yake yi da Abdul Aziz limamin Jan masallaci a Islamabad.

Mr Zaki da sauran masu rajin kare hakkin bil Adama sun shigar da kara a kotu inda suke tuhumar malamin da tunzura jama'a a kan 'yan Shia marasa rinjaye a Pakistan.