Ana zaben shugaban kasa a Philippines

Hakkin mallakar hoto REUTERS
Image caption Ana gudanar da zaben shugaban kasa a Philippines

Al'umar Philippines na gudanar da zaben shugaban kasa, inda ake sa ran wani maganannen Magajin-gari, wato Rodrigo Duterte zai kasance shugaban kasa.

A halin da ake ciki dai shi ne mafi tagomashi ko farin-jini a tsakanin sauran abokan hamayyarsa mutum hudu, kodayake ya yi zargin cewa gwamnatin kasar na shirin tabka magudi wajen ganin dantakaranta, Mar Roxas ya ci zaben.

Rodrigo Duterte dai ya samu dimbin magoya baya a yakin neman zabensa.

Rahotanni sun ce Rodrigo Duterte mutum ne mai yawan takaddama, ba ya shakkar magana, kuma manufofinsa cike suke da tawili.

Ya dai yi barazanar halaka dubban masu aikata miyagun laifuka, ya kuma ce zai taka kowa tamkar mai kama-karya idan 'yan majalisar dokokin kasar suka ki yi masa biyayya.

Har wa yau ya shaida wa magoya bayansa cewa kula da Farka ko Farekunsa ba za ta zame wa gwamnati dawainiya ba, saboda gidajen da yake ajiye su ba masu tsada ba ne.