Mutum 20 sun mutu a zaftarewar kasa a Rwanda

Mutane kusan 20 sun mutu sakamakon zaftarewar kasa a Rwanda bayan ruwan sama kamar da bakin kwarya a arewacin kasar.

An sami aukuwar munanan zaftarewar kasa a Rwanda a cikin wannan shekarar.

Kimanin mutane 70 suka mutu a wuraren da suka hada Kigali babban birnin kasar.

Rwanda kasa ce mai cinkoson jama'a wadda ke da tsaunuka da koramu inda kuma zazzayar kasa ta zama babbar matsala.

A shekarun baya bayan nan gwamnatin ta matsar da wasu mutane daga wuraren da ake gani suna da matukar hadari.