Manyan kamfanonin Burtaniya na fuskantar hari

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Satar bayanai ta kwamfuta

A cikin shekarar da ta wuce an yi wa kashi biyu bisa ukun manyan kamfanonin Burtaniya satar bayanai ta intanet, kamar yanda wani bincike da gwamnati ta gudanar ya nuna.

Kamfanin da ya gudanar da binciken, wato Cyber Security Breaches Survey ya bayyana cewa ana amfani da cutar kwamfuta ne da wasu manhajojin cutarwa wajen satar bayanan manyan kamfanonin.

Ya kara da cewa kashi bisa hudun kamfanin na fuskantar irin wannan harin ko satar bayanan akalla sai daya a kowane wata.

Ministan tattalin arziki a bangaren fasahar zamani, Ed Vaizey ya ce akwai bukatar a samar da kariya ga harkokin kasuwanci da kuma bayanan sirrin kamfanoni, kasancewar wani lokaci satar bayanan na haddasa asarar miliyoyin dala.

Binciken ya nuna cewa za a iya kare kamfanoni daga kashi bakwai a cikin hare-hare goma da akan kai musu, amma abin takaici shi ne kashi daya bisa biyar din kamfanonin kasar ne kadai suka san hadarin da ke tattare da buda sirri ga na waje.

A halin da ake ciki dai gwamnatin Burtaniya ta yi shirin kashe Fam £1.9bn a cikin shekara biyar masu zuwa wajen kare sirrin kamfanoni da harkokin kasuwanci.