An jinkirta tsige shugabar Brazil

Hakkin mallakar hoto AFP

A Brazil shirin tsige shugabar kasar, Dilma Rousseff ya samu babban koma baya.

Mai riƙon mukamin kakakin majalisar wakilan kasar, ya soke wata ƙuri'a da aka kaɗa a watan Afrilu, wacce ta baiwa majalisar dattawa damar ci gaba da shirin tsige shugabar Kasar.

Ya kuma yi kiran da a gudanar da sabuwar ƙuri'a.

Mr Maranho ya ce an tafka kurakurai a ƙuri'ar da aka kaɗa a watan Afrilu game da batun.

Kakakin majalisar ya ce, bai kamata a ce mambobin majalisar wakilan kasar sun bayyana matsayinsu kafin a kada kuri'ar ba.

Kuma bai kamata a ce shugabannin jam'iyya sun nunawa mambobinsu yadda za su kada kuri'ar ba.

An dai shafe makonni ana kai ruwa rana a Brazil dangane da yunƙurin tsige shugabar kasar.