Ana cece-kuce kan rijistar zaben Ghana

Hakkin mallakar hoto Chris Stein AFP

Manyan jam'iyyun kasar Ghana, NDC mai mulki da kuma jam'iyyar adawa ta NPP suna zargin juna da yi wa baƙi 'yan kasashen waje da kuma wadanda shekarunsu ba su kai yin zabe ba rijista.

A ranar Lahadi ne dai hukumar zaben kasar ta kammala rijistar masu zaben wanda za a gudanar a watan Nuwamban bana.

Ta yi rijistar ne ganin cewa kananan yaran da a baya ba su kai shekarun zabe ba, yanzu sun kai.

Jam'iyyun biyu sun bukaci hukumar ta yi bincike kan wadannan zarge-zarge.