Kebbi: An sace wa manoma amfanin gona

Hakkin mallakar hoto Kebbi Govt
Image caption A cikin watan Nuwambar bara ne shugaba Muhammadu Buhari ya ƙaddamar da shirin bai wa manoman shinkafa tallafin bashi

A jihar Kebbi da ke arewacin Najeriya, manoman shinkafa a ƙaramar hukumar Argungu sun wayi gari da wani tashin hankali, bayan da wasu daga cikinsu suka taras an girbe, tare da sace ƙaukacin shinkafar da suka noma a bana.

Lamarin dai kamar yadda wani manomi ya shaida wa BBC ya sa wasu manoman da satar bata fada kansu ba suka duƙufa wajen gadin gonakinsu a ranar Litinin.

Wasu kuwa tuni suka fara girbe nasu amfanin gonar suna mayarwa gida domin tsoron ƙara faruwar hakan.

A cikin watan Nuwambar bara ne shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ƙaddamar da shirin bai wa manoman shinkafa na ƙasar tallafin bashin naira biliyan 20 a jihar Kebbi, don bunkasa noman shinkafar.

Ga dai rahoton Bilkisu Babangida:

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti