Nijar: Shugaban kasa zai rage masu bada shawara

Hakkin mallakar hoto

A jamhuriyar Niger shugaban kasar, Alhaji Mahamadou Issoufou zai rage yawan mashawarta.

Shugaban kasar zai rage mashawarta da wasu wakilai a fadarsa, da fadar shugaban majalisar dokoki, da kuma ofishin firayim minista.

Za a dau wannan mataki ne dai da nufin tsuke bakin aljihun gwamnati.

Mataimakin sakataren yada labarai na jam'iyar PNDS Tarayya, Alhaji Assoumana Mohammadou wanda kuma tsohon mashawarci ne a fadar shugaban kasa ya sanar da cewa aikin mashawartan ya kare domin an cimma bukatun da ake so a cimma.

Masu lura da al'amura a jumhuriyar ta Nijar na cewa, matakin ba zai rasa nasaba da shirin tsuke bakin aljihun gwamnati da shugaban kasar ya bullo da shi.