Nigeria: Me kasafin kuɗin bana ya ƙunsa?

Hakkin mallakar hoto Presidency

A ƙarshen makon jiya ne shugaban Nigeria, Muhammadu Buhari ya sanya hannu akan kasafin kuɗin bana.

Gwamnati ta fayyace wasu muhimman abubuwa da kasafin kuɗin ya ƙunsa:

  1. Za a samar da malaman makaranta masu shaidar karatun digiri 500,000
  2. Za a riƙa samar da tallafin naira 5000 kowanne wata ga mutane da suka kai miliyan guda masu fama da fatara.
  3. Za a samar da rancen jari ga mata 'yan kasuwa miliyan guda, da masu sana'ar hannu 460,000.
  4. Za a bada kudin tallafin karatu ga ɗaliban jami'a dake nazarin lissafi, da kimiyya da fasaha.
  5. Za a haɗa kai da jihohi wajen samar da tsarin ciyar da 'yan makaranta miliyan 5 da rabi kowacce shekara.
  6. Za a yi gyara ga dokar mallakar fili domin sauƙaƙa mallakar fili ga jama'a.
  7. Za a samar da fili mai faɗin hekta 5 zuwa goma a kowacce jiha domin samar da gidaje masu sauƙin kuɗi.
  8. Za a gyara ɗakin shan magani ɗaya a kowacce mazaɓa, wato mazaɓu 10,000 a duk faɗin Nigeria.