An kori ma'aikatan BBC daga Koriya ta arewa

Image caption Ma'aikatan BBC sun je Koriya ta arewa ne don ba da labarin babban taron jam'iyya mai mulkin kasar.

Mahukunta a Koriya ta arewa sun kame ayarin ma'aikatan BBC, kuma suna shirin fatattakarsu daga kasar.

Ana shirin fitar da wakilin BBC Rupert Wingfield-Hayes da mai daukar hoto ko Kemaraman da kuma jagoransu daga Pyongyang bayan an dauko su daga filin jirgin saman kasar an kai su masauki.

An dai shafe sa'a takwas ana yi wa Rupert Wingfield-Hayes tambayoyi, kana aka bukace shi da ya nemi gafarar mahukunta.

Babban Sakataren kwamitin sulhu na kasar Koriya ta arewa, O Ryong Il ya ce wakilin BBC ya jirkita bayanai, ya kuma aibanta gwamnatin kasar da kuma shugaba Kim Jong-un.

A halin da ake ciki dai har an garzaya da ayarin ma'aikatan BBC zuwa filin jirgin sama.

Ayarin dai ya je Koriya ta arewa ne don ba da labarin babban taron jam'iyya mai mulkin kasar.