A kimiyyance tsirrai 390,900 ake da su a duniya

Hakkin mallakar hoto Getty

Masanan kimiyya sun ƙiyasta cewa akalla tsirrai 390,900 duniya ta ƙunsa.

Wani bincike da aka gudanar ya bada sabon lissafi kan yawan tsirrai da ake da su a duniya a kimiyyance.

Cibiyar bincike kan tsirrai ta Royal Botanic Gardens ita ce ta sanar da hakan bayan ta gano wasu sabbin tsirrai 2,034 a 2015, da kuma ta yi bincike a kansu.

Binciken ya sanar da cewa, kashi 21 cikin 100 na waɗannan tsirrai su na da hatsari.

Wasu daga cikin tsirran na iya barazana ga sauyin yanayi, wasu kuma na iya haddasa cututtuka.

Wasu kuma na iya kasancewa abinci, ko kuma su samar da makamashi ko magunguna.