Zaftarewar ƙasa ta kashe mutum 49 a Rawanda

Hukumomi a ƙasar Rwanda sun ce aƙalla mutum 49 ne suka mutu sakamakon zaftarewar ƙasa, bayan saukar ruwan sama mai ƙarfi a ranakun Asabar da Lahadi.

Yawancin wadanda suka mutun dai a arewacin ƙasar suke.

Yara ƙanana da kuma dattawa na cikin wadanda suka mutu.

Hukumomi sun ce daruruwan gidaje sun rushe.

Rwanda dai ƙasa ce mai yawan jama'a, da tsaunuka da kwazazzabai inda zaizayar ƙasa ke matuƙar damun ta.

A 'yan shekarun nan gwamnatin Rwanda na ƙarfafawa mutane gwiwar su rinka barin yankunan da ake ganin suna da matukar hatsari.