'Ma'anar kalaman Cameron kan Nigeria'

Hakkin mallakar hoto AFP

Shugaban Nigeria, Muhammadu Buhari ya ce gwamnatinsa ta yi matukar kaduwa da kalaman da firaiministan Birtaniya, David Cameron ya yi, cewa Najeriya na gaba-gaba wajen cin hanci da rashawa a duniya.

Mai magana da yawun shugaban kasar, Garba Shehu, ya ce watakila Mista Cameron din yana magana ne kan kaurin sunan da kasar ta yi kafin shugaba Buhari mulki.

A ranar Talata ne aka dauki hoton bidiyon Firai ministan na Birtaniya, yana wata katobara, inda yake shaidawa Sarauniyar Ingila cewar shugabannin wasu kasashen da suka fi bala'in cin hanci da suka hada da Najeriya za su halarci taron kolin da zai karbi bakunci, a ranar Alhamis, game da yaki da cin hanci.

Ga karin bayanin da Garba Shehu ya yi wa Haruna Tangaza:

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti