Pakistan: An ceto Gilani daga hannun IS

Gwamnatin Pakistan ta ce an ceto ɗAn tsohon Firai ministan Pakistan Ali Haider Gilani, a Afghanistan shekaru uku bayan sace shi da aka yi.

An ceto Ali ne a wani samamen haɗin gwiwar dakarun Amurka da Afghan a lardin Ghazni da ke kudancin ƙasar.

'Yan uwa da abokai masu taya murna sun taru a wajen gidan danginsu a birnin Multan da ke Pakistan.

Wasu waɗanda ake zargin 'yan bindiga ne a Multan suka sace Gilani a shekarar 2013, a yayin da ya ke yaƙin neman zaben majalisa.

A shekarar da ta gabata ne mahaifinsa ya ce waɗanda suka sace shi sun buƙaci a sako 'yan kungiyar Al-Qeada da ke gidan yari idan yana so a sako ɗansa.