Trump zai bar Sadiq Khan ya je Amurka

Image caption Trump ya ce dokar hana Musulmi shiga Amurka ba za ta shafi Sadiq Khan ba.

Mutumin da ake sa ran zai tsawaya jam'iyyar Republican takarar shugabancin Amurka, Donald Trump, ya ce zai bar sabon Magajin birnin London, Sadiq Khan ya ziyarci kasar idan ya lashe zabe.

Trump dai ya yi ƙaurin suna wajen ƙin jinin Musulmi, inda ya ce zai hana su shiga kasar idan ya ci zaben shugabancin Amurka.

Sai dai a wata hira da ya yi ya ce "Akwai mutanen da dokar [hana Musulmi zuwa Amurka] ba za ta shafa ba".

Mista Trump ya ce ya yi matukar farin ciki da Sadiq Khan ya zama Magajin birnin London.

Da ma dai Sadiq Khan ya ce ba zai kai ziyara Amurka ba idan Trump ya ci zabe sakamakon haramcin da ya yi wa Musulmi na shiga kasar.