Illar kiba ga lafiyar mutane ta ragu sosai

Hakkin mallakar hoto Getty

Wani sabon bincike da aka wallafa a wata mujalla ta kungiyar likitocin Amurka, ya nuna cewa a halin yanzu kiba bata barazana ga lafiya kamar yadda ta yi shekaru 40 da suka wuce.

A Denmark ne wasu likitoci suka yi bincike kan tsawo da kiba da alakarsu da mutuwa a lokuta uku daban-daban a kasar, a farkon shekarun 1970.

Likitocin sun gano cewa yanzu kiba ba ta kai wa ga yin kisa da wuri kamar yadda take yi a baya, kuma suka ce an samu wannan nasara ne sakamakon cigaban da sashen kiwon lafiya ya samu a yanzu, musamman magungunan cututtuka da aka samu irin na yawan kitse da hawan jini.

Ko a kwanann baya ma Biritaniya ta sanya haraji kan kayan zaki a kasar, domin rage handamarsa da al'ummar ke yi kuma yake sanadin cututtuka da ke da alaka da yawan kitsen da ke barazana ga lafiyar al'ummar kasar.