'Karancin riga-kafin cutar shawara babbar illa ce'

Image caption Kwayoyin cutar shawara

Masana kimiyya a Amurka sun yi gargadin cewa karancin da ake fuskanta na allurar rigakafin cutar shawara ta yellow fever, na iya janyo wata babbar barazana ga kiwon lafiya a duniya.

Mutane sama da 270 ne suka mutu a kasar Angola da ke kudancin Afrika, tun bayan barkewar annobar cutar a watan Disamba.

Yanzu haka dai an ce cutar na ci gaba da yaduwa, duk da matakin yi wa jama'a rigakafi.

Don haka ne masana kimiyyar suka yi kira ga hukumar lafiya ta duniya wato WHO ta dauki matakan gaggawa domin shawo kan lamarin.