Yara na mutuwa a barikin sojin Nigeria — Amnesty

Image caption Sojojin Najeriya suna tsare da mutane da dama

Ƙungiyar kare haƙƙin bil Adama ta Amnesty International ta ce akalla mutane 149 ne, da suka hada da ƙananan yara, suka mutu a 2016, a barikin sojin Najeriya.

Amnesty ta ce mutanen sun mutu ne a yayin da suke a tsare a barikin sojoji da ke arewa maso gabashin ƙasar, inda hukumomi ke cigaba da fafatawa da 'yan ƙungiyar Boko Haram.

A wani rahoto da ta fitar ranar Laraba, ƙungiyar ta yi zargin cewa ana tsare da mutanen ne a cikin wani mummunan hali da kuma ƙuntatawa.

Rahoton ya ce akalla ƙananan yara 11 ne suka mutu da suka hada da jarirai sakamakon cututtuka da yunwa da kishirwa da kuma harbin bindiga.

Amnesty ta ƙara da cewa akwai mutane da ake tsare da su a barikin na Giwa fiye da 1,200, a inda kungiyar ta nemi da a saki mutanen sannan kuma a rufe wurin.

Kawo yanzu dai babu wani martani da rundunar sojin ta mayar.