India: 'Yar shekaru 72 ta haihu

Image caption Wannan ta haihu ne tana da shekaru 70

A India wata mace mai shekaru saba'in da biyu ta yi haihuwar fari bayan anyi mata aikin dake haɗa ƙwan halitta wato IVF.

Ita dai matar mai suna Daljinder Kaur, wadda mijinta yake da shekaru saba'in da tara, ta haifi ɗa namiji ne cikin watan jiya.

Ta shafe shekaru biyu ana yi mata aikin dake habaka kwan halitta a wani asibiti da ya ƙware a wannan fanni a jihar Haryana dake arewacin kasar.

Dattijuwar ta faɗawa manema labarai cewa, cikin shekaru arba'in da shida na zaman aure sun fidda rai da samun haihuwa.

Amma wannan fa ba shi ne irinsa na farko ba a India, inda koda a shekara ta 2008 wata mai shekaru saba'in ta samu karuwa ta wannan hanya a jihar Uttar Pradesh.