IS: Bam ya halaka mutane fiye da 60

Jami'ai a Kasar Iraqi sunce wani bam da aka dasa a cikin mota kusa da wata kasuwa mai cunkuso a Bagadaza ya halaka mutane fiye da 60.

Wannnan shine hari mafi muni da aka kai a birnin a 'yan shekarun nan.

An kuma jikkata mutane da dama a fashewar bam din, wanda ya tashi a lardin birnin Sadr inda musulmi 'yan shi'a suka fi yawa.

Mayakan IS dai ta dauki alhakin kaddamar da harin.