Jami'an China ba su da da'a —Sarauniya

Hakkin mallakar hoto
Image caption Sarauniya Elizabeth tana tattaunawa da babbar jami'ar yan sanda a wurin liyafa

An nadi sarauniya Elizabeth ta Birtaniya a hoton bidiyo tana cewa jami'an China sun nuna rashin da'a a ziyarar da shugaba Xi Jinping ya kai kasar a shekarar da ta gabata.

A ranar Talata ne dai Sarauniyar ta yi wadannan kalamai ne a lokacin da ta ke wata tattaunawa da wani babbar jami'ar yan sanda a wurin liyafar da aka yi a lambun fadar Buckingham a kan irin yadda suka yiwa jakadan Birtaniya da ke China.

Wannan dai yazo ne bayan an jiyo Firai ministan Birtaniyan David Cameron yana cewa Afghanistan da Nigeria sun yi kaurin suna a "cin hanci da rashawa".

Masauratar dai ta ce an samu nasara sosai a ziyarar da shugaban China din ya kai Birtaniya a bara.