Birtaniya na cin gajiyar kuɗaɗen sata — Transparency

Image caption An dai dauko bidiyon da David Cameron yake fadawa sarauniya Elizabeth, ne a boye.

Ƙungiyar Transparency International mai yaƙi da cin hanci da rashawa ta ce Burtaniya da wasu yankunan da ke ƙarƙashinta da ke ƙetare, wurare ne da ake ɓoye kuɗaɗen da aka samu ta hanyar almundahana.

Shugaban ƙungiyar, Cobus de Swardt, ne sanar da hakan a lokacin da yake mayar da martani kan kalaman da firaiministan Birtaniya, David Cameron ya yi cewa Najeriya da Afghanistan sun kowace ƙasa rashawa da cin hanci, a duniya.

Sai dai kuma mista Swardt ya amince da cewa Najeriya da Afghanistan sun yi ƙaurin suna wajen cin hanci da rashawa, lamarin da har yanzu ba a kawo ƙarshensa ba.

To amma kuma Swardt ya buƙaci ƙasashe kamar Birtaniyar da su buɗe sabon babi na yaƙi da cin hanci da rashawa a ƙasashen.