BBC za ta yi gagarumin sauyi

Gwamnatin Burtaniya ta bada sanarwar yin gagarumin sauyi a yadda ake tafiyar da kafar yada labarai ta BBC.

Da yake magana a majalisar dokoki, sakataran raya al'adu na Biritaniya, John Whittingdale, ya ce za a soke hukumar dake sa ido kan ayyukan BBC, a maye gurbinta da wata hukumar, wadda BBCn zata zabi mambobinta, da kanta ba tare da sa hannun gwamnati ba.

Ya ce a duk fadin duniya ana daukar sashen BBC dake watsa shirye shiryensa ga kasashen duniya a matsayin wani jagaba wajan bada sahihin labarai da babu son zuciya ciki.

Mr Whittingdale ya ce za'a kare tare da ninka kudadan da ake tafiyar da sashen BBC dake watsa shirye shiryensa ga kasashen duniya, wanda ya kai sama da fan miliyan dari biyu da hamsin.