BH: Yadda mutane suka jikkata a Maiduguri

Hakkin mallakar hoto Isa Gusau
Image caption Gwamnan Borno Kashim Shettima, inda ya ke duba marasa lafiyar da bam ya jikkata a baya, a asibitin jihar.

Harin ƙunar baƙin wake da ake zaton 'yan Boko Haram ne suka kai ya jikkata mutane 19, a Maiduguri, babban birnin jihar Borno.

Lamarin dai ya faru ne yayin da wani ɗan ƙunar baƙin wake ya tayar da bam a ƙofar shiga sakatariyar gwamnatin jahar ranar Alhamis.

Mai magana da yawun gwamnan jihar, Usman Kumo, ya shaida wa BBC cewa maharin da wani jami'in tsaro daya sun mutu a harin.

Usman kuma ya kara da cewa zuwa yanzu mutane 19 ne suka samu raunuka kuma tuni aka garzaya da su zuwa asibiti.

Ya ce dan kunar bakin waken ya yi badda-kama ne a matsayin ma'aikacin jiha da za a tantance.

''Da yake ana tantance ma'aikatan jiha a sakatariyar, sai shima wannan mutumi ya zo ya bi layin har da fayil dinsa a hannu, kawai sai da layi ya zo kansa sai ya tayar da bam din,'' in ji Kumo.

Ko a ranar Laraba ma wani dan kunar bakin wake ya yi yunkurin kai hari birnin na Maiduguri, amma sojoji suka dakile harin.

Wani wanda yana wurin al'amarin ya afku ya zanta da Ahmad Abba Abdullahi a wannan hirar:

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti