'Zan ƙwato haƙƙina kan tsigeni da aka yi'

Shugabar ƙasar Brazil mai barin gado Dilma Rousseff, ta sha alwashin neman haƙƙinta iyakar iyawarta a shari'ance kan tsigeta da aka yi.

An dakatar da Ms Rousseff ne bayan da majalisar dattijan ƙasar ta kada ƙuri'ar tsigeta, amma ta tsaya kai da fata cewa ba ta aikata kowanne laifi ba.

Ta sha maimaita cewa tsigeta na nufin juyin mulki.

A yanzu haka mataimakinta Michel Temer, shi ne yake rikon ƙwarya.

Tuni ya bayyana sunayen 'yan majalisar ministocinsa da suka haɗa da ministan kudi Henrique Meirelles, wanda shi ne gwamnan babban bankin kasar lokacin da aka samu haɓakar tattalin arzikin da ba a taba ganin irinta ba a Brazil a baya-bayan nan.